Isa ga babban shafi

Amurka ta ware Dala miliyan 50 saboda zaben Najeriya

Amurka ta ware Dala miliyan 50 domin tallafa wa  Najeriya gudanar da zaben shugaban kasa a shekara maai zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Amurka Joe Biden yayin wata ziyara da Buhari ya kai Amurka lokacin shugaba Barack Obama © Presidency of Nigeria
Talla

Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden har da horas da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula baya ga taimakawa wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.

Jakadan Amurka, Mista Will Stevens, shi ne ya sanar da tallafin a wannan Litinin a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a yayin wani taron horas da ‘yan jarida wanda Cibiyar Horas da Yada Labarai ta Yammacin Afrika WABMA ta shirya.

Mista Stevens ya ce, gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumarta ta Raya Kasashe Masu Tasowa USIAD, domin ganin an kidaya kuri’ar kowa da kowa a yayiin zaben na 2023 a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.