Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya 2023: Ku zabi duk wanda kuke so - Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari  ya shaida wa ‘yan kasar su zabi wanda suke so daga kowace jam’iyyar siyasa a yayin zaben shekarar 2023.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Julien de Rosa
Talla

Ya ce babu wanda za a bari ya raba kudi ga ‘yan jagaliyar da za su yi barazana ga masu zabe a dukkanin mazabu.

Shugaba Buhari yana bayani ne a birni Landan a ranar Laraba, bayan da yay a kammala wata ganawa da sarkin Ingila Charles na 3 a fadar Buckingham.

Buhari ya ce burinsa shi ne ‘yan Najeriya su yarda cewa gwamnatinsa tana ganin girmansu, kuma tana mutunta su, yana mai cewa abin da yake so su tuna kena bayan ya sauka daga karagar mulki.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC da dan takararta, Bola Ahmed Tinubu ne za su lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa.

Buhari ya ce ‘APC ta yi dacen samun Tinubu a matsayin dan takaran shugaban kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.