Isa ga babban shafi

Najeriya: Buhari ya tabbatar da cewa za a gudanar da sahihin zabe a 2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na gudanar da karbabben zabe a shekara mai zuwa domin zabo wanda zai maye gurbin sa a matsayin shugaban kasa.

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Buhari ya bayyyana haka ne ga taron majalisar Dinkin Duniya dake gudana a New York, bayan ya koka akan yadda shugabannin wasu kasashe ke sauya kundin tsarin mulki domin ci gaba da zama a karaga.

Shugaban Najeriyan wanda ya jinjinawa kawayen kasar akan irin gudumawar da suke bata wajen ganin dimokiradiya ta zauna da gindinta, yace daya daga cikin abin tarihin da zai baiwa jama’ar kasar, shine gudanar da karbabben zabe a watan Fabarariru mai zuwa.

Buhari ya shaidawa taron Majalisar cewar, a irin wannan lokaci a shekara mai zuwa, wani sabon shugaban kasa ne zai tsaya a gaban su domin gabatar da jawabi a madadin Najeriya.

A watan Mayu mai zuwa shugaban ke kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8, wanda ya fara tun daga shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.