Isa ga babban shafi

Babu inda aka dasa bam a Abuja-Yan Sanda

Rundunar yan Sandan Najeriya tace babu gaskiya a cikin labaran da ake yadawa cewar an dasa bama bamai a sassan birnin Abuja a wani yunkuri na kai harin ta’addanci a birnin.

Wani yanki a Abuja, babban birnin Najeriya.
Wani yanki a Abuja, babban birnin Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mai magana da yawun Yan Sandan kasar Olumuyiwa Adejobi wanda yayi watsi da rahotannin, yace abin takaici ne yadda ake yada su da zummar tada hankalin jama’ar Abuja da kuma Najeriya baki daya.

Adejobi ya sake jaddada cewar har ya zuwa wannan lokaci birnin Abuja na cikin kwanciyar hankali, kuma babu wata barazanar da yake fuskanta domin jami’an tsaro daga bangarori da dama na aikin su na kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

Kakakin ya bukaci mazauna Abuja da sauran yan Najeriya da su ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

Ko a jiya sanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su ci gaba da harkokin su na yau da kullum saboda yadda jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da harkokin su na tabbatar da tsaro a sassan kasar.

Kasashen Amurka da Birtaniya suka fara gabatar da gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci birnin da kuma bukatar yan kasashen su da suyi taka tsan tsan, yayin da daga bisani wasu kasashe suka bi sahu wajen gargadin jami’ansu dake aiki a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.