Isa ga babban shafi

Kifewar kwale-kwale ya kashe mutum 15 a jihar Sokoton Najeriya

Akalla mutane 15 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Wani kwale kwale dauke da mutane
Wani kwale kwale dauke da mutane REUTERS/Michalis Loizos
Talla

Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a lokacin da wadanda abin ya shafa ke tafiya wani kauye mai makwabtaka domin halartar bikin Moulud Nabiy, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Shugaban karamar hukumar, Aliyu Abubakar Dantani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka daban-daban.

Ya ce, “Su 25 ne lokacin da jirgin ya kife amma an ceto 10 daga cikinsu da ransu. Sun fito ne daga kauyuka hudu daban-daban, suka hadu a daya daga cikin kauyukan, daga nan suka shiga kwalekwale domin nufa wurin bikin maulidin.

“Suna kan hanyarsu ta zuwa wani kauye domin bikin Maulidi na shekara amma kwale-kwalen ya kife kafin su isa inda suke,” in ji Dantani.

"Mutane 15 ne suka nutse amma daga baya an gano gawarwakinsu kuma an binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."

A cewar Dantani, hudu daga cikin wadanda suka mutun sun fito ne daga kauyen Gidan Raket, uku daga Gidan Dawa, bakwai daga Sabon Garin Sullubawa, sai kuma yarinya daya daga Tsohon Garin Sullubawa.

Game da alkawarin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi a shekarar 2021 na samar da rigunan ceto a kauyukan da ke kusa da karamar hukumar, shugaban ya ce "har yanzu ana kan hanya."

Karamar hukumar Shagari dai ta shafe shekaru tana fama da hadurran jiragen ruwa. Ko a shekarar 2021, wani jirgin ruwa da ya kife da bakin daurin aure, ya kashe mutane 13 wadanda galibinsu mata da yara ne a kauyen Ginga.

A watan Afrilun bana, wasu matasa 29 da suka hada da wata amarya sun mutu a hatsarin kwale-kwale a kauyen Gidan Magana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.