Isa ga babban shafi

Najeriya na kashe dala miliyan 10 wajen ciyar da dalibai miliyan 10 -Ngige

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na kashe tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 10 a karkashin shirinta na ciyar da yara ‘yan makarantun firamare miliyan 10 da ke sassan kasar a wani yunkuri na karfafa gwiwar yaran don mayar da hankali a karatu.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dr Chris Ngige.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Dr Chris Ngige. Daily Post
Talla

Ministan kwadago da samar da ayyukanyi na Najeriyar, Chris Ngige wanda ke sanar da wannan alkaluman yayin karbar bakoncin jakadar Amurka a kasar Mary Leornard a ofishin sa da ke Abuja, ya ce matakin na da nufin magance matsalolin yaran.

Mininistan ya ce gwamnatin Najeriya ta samar da shirin ciyar da yara a makarantu ne don magance bautar da su a zamanance da ake yi da sunan aikatau ta hanyar mayar da su makarantu.

Ngige ya ye gwamnati ta samar da shirye-shiryen ne domin yaki da talauci, da kuma kwadaitar da yara karatu baya ga kawar da matsalar bautarwa ga yaran musamman a karkara.

Ministan ya ce a yanzu akwai yara ‘yan makaranta kimanin miliyan goma da ke cin gajiyar wannan shirin a sassan Najeriya musamman a yankunan karkara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.