Isa ga babban shafi

Buhari ya amince da ware naira biliyan 470 a kasafin badi don inganta jami’o'i

Bayan Kwashe watanni 7 malaman jami’oin Najeriya na yajin aiki domin tilastawa gwamnatin kasar kara kudaden da gwamnati ke kashewa wajen bunkasa jami’oin kasar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware naira biliyan 470 a kasafin kudin shekara mai zuwa domin inganta jami’oin.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari © lailasnews
Talla

Yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a gaban Majalisar kasa, shugaba Buhari ya ce za’a ware naira biliyan 470 domin gudanar da manyan ayyukan bunkasa jami’oin gwamnatin tarayya daga cikin naira triliyan 20 da miliyan dubu 15 da gwamnatin zata kashe a shekara mai zuwa.

Kungiyar malaman jami’oin ta ASUU ta bukaci ware naira triliyan guda da miliyan dubu 200 ne domin kashewa jami’oin mallakar gwamnati, amma sai gwamnatin ta ce ba za ta iya ba.

Kafin gabatar da kasafin, gwamnatin ta yi tayin ware naira biliyan 150 amma kungiyar malaman taki amincewa.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewar gwamnati ba za ta iya daukar nauyin bukatun jami’o'in ita kadai ba, saboda yawan su, inda ya bukaci shugabannin jami’o'in da su duba wasu hanyoyin samun kudade da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.