Ci gaba da kasancewar jami'o'in Najeriya a kulle ya na kona min zuciya- Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya na matukar samun tashin hankali a game da yadda ake ci gaba da kulle jami'o'in kasar sakamakon yajin aikin kungiyar ASUU ya na mai rokon malaman jami’o’in kasar da su bude makarantu.
Wallafawa ranar:
Shugaban wanda ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai a yayin bikin cikar kasar shekaru 62 da samun yancin kai, ya bukaci malaman jami’a da ke yajin aiki su koma ajizuwa, a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don lalubo masalaha.
Buhari ya ci gaba da cewa yana jin kuna a cikin zuciyarsa a kan yadda yajin ya ke kawo cikas a kan ilimi mai zurfi a kasar, yana mai shawartar malaman jami’an da su bari a yi amfani da iya abin da Allah ya huwace wa gwamnatin tarayya wajen warware matsalolinsu.
Yajin aikin da malaman jami’a a Najeriya ke yi a halin yanzu ya gurgunta harkokin karatu tun da suka fara shi a ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
Tun da aka fara wannan yajin aikin ne ‘yan Najeriya da dama ke ta magiya a game da batun warware matsalar, a yayin da kungiyar daliban kasar suka gudanar da jerin gangami don tabbatar da an samu mafita, amma lamarin ya ci tura.
Malaman jami’an suna neman a kyautata yanayin karatu ga dalibai, karin kudaden tafiyar da jami’o’in a kan wanda gwamnati ke samarwa da kuma karin albashi, kamar yadda yake kunshe a yarjeniyoyi da dama da suka kulla da gwamnatin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu