Isa ga babban shafi

Takaitaccen jawabin shugaba Buhari a bikin tunawa da ranar 'yancin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce tun bayan zaben sa a karon farko cikin shekarar 2015, gwamnatin sa ta zo da alkawura  da dama a bangaren bunkasa tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa da yaki da ta’addanci, lamarin da ya ce ya taimakawa kudurin gwamnatin sa wajen fitar da mutane miliyan 100 daga talauci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Akan batun yaki da cin hanci da rashawa, Buhari ya ce gwamnatin sa ta zo da tsare-tsare da dama da ya sanya ta samun goyon baya daga kasashen ketare da ya taimaka wajen dawo da kudade da dama da aka sace aka kai kasashen waje.

Hakananan Buhari ya tabo batun kara yawan wadanda ake hukuntawa bisa zargin su da cin hanci da rashawa, da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen dakatar da duk wasu hanyoyi da ke bada damar cin hanci da rashawa a sassan kasar.

A bangaren tsaro kuwa, Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatin sa, ta yi aiki tukuru wajen yakar 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin kasar da tsagerun Niger Delta a kudu masu kudancin kasar da rikicin addini da sauran batutuwan da ke kawo barazana ga zaman lafiya.

Shugaba Buhari ya tabo batun farfado da tattalin arzikin kasar, musamman yadda ya samar da tsarin asusun bai daya wato TSA da rage kudade barkatai da ya taimakawa kasar wajen fitowa daga cikin matsin tattalin arziki cikin sauri.

Har wayau, shugaban ya ce gwamnatin sa ta mayar da hankali a bangaren noma da tallafawa masu kanana da matsakaitan sana’oi ta hannun babban bankin kasar CBN, lamarin da ya samar da dimbin guraban ayyukan yi ga al'ummar kasar.

A bangaren zabe kuwa, shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dukkanin nasarorin da ake son cimmawa ba zai samu ba sai da ingantacciyar gwamnati, don haka ya ce gwamnatin sa na kokarin tabbatar da gudanar da zabe mai inganci.

Muhammadu Buhari ya ce idan aka yi la’akari da nasarorin da aka samu na gudanar da ingantaccen zabe a jihohin Anambra da Ekiti da kuma Osun da wasu dai-daikun zabukan cike gurbi, a bayyane ya ke ga jama'a gano irin ingancin da za a samu a babban zaben kasar na shekara mai zuwa.

Shugaba Buhari bai kammala jawabin sa ba har sai da ya taba batun alakar kasar da kasashen waje, inda ya ce Najeriya ta amfana sosai da kyakyawar alakar da ke tsakanin ta da kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.