Isa ga babban shafi

INEC ta soke rajistar masu zabe a Najeriya

Hukumar Zaben Najeriya ta sanar da soke rajistar masu kada kuri’u sama da miliyan guda daga cikin na mutane sama da miliyan 2 da rabi da suka yi rajistar tsakanin 28 ga watan Yunin bara zuwa 14 ga watan Janairun wannan shekara saboda rashin ingancinsu.

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. © The Guardian Nigeria
Talla

Kwamishinan Hulda da Jama’a da kuma ilmantar da mutane kan shirin zaben Najeriya Festus Okoye ne ya sanar da daukar wannan mataki, sakamakon abin da ya kira samun mutanen da suka yi rajistar sama da guda, wanda ya sabawa dokokin zaben kasar.

Okoye ya ce za su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin akan mutanen da suka yi rajistar daga watan Fabarairu zuwa Yulin wannan shekara, domin tantance rajistar da kuma tsaftace ta baki daya.

Kwamishinan ya ce, daga karshen watan Oktoba mai zuwa za su fara bai wa 'yan Najeriya katin zaben na din-din-din kamar yadda suka yi alkawari.

Okoye ya ce da zaran sun kammala aikin tsaftace rajistar, za su sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki da kuma yawan yan Najeriyar da sunayen su ke cikin rajistar.

A watan Fabarairu mai zuwa ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da kuma gwamnonin kasar kamar yadda jadawalin zabe ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.