Isa ga babban shafi

Hadarin wata tankar mai ya haddasa gobarar da ta kone gidaje 10 a Ogun

Akalla gidaje 10 ne suka kone kurmus a karamar hukumar Ifo da ke jihar Ogun ta kudancin Najeriya bayan da wata tanka makare da man fetur ta kama da wuta da safiyar yau asabar.

Gobarar sanadiyyar hadarin tankar mai ba sabon abu ba ne a Najeriyar.
Gobarar sanadiyyar hadarin tankar mai ba sabon abu ba ne a Najeriyar. STRINGER / AFP
Talla

Rahotanni sun ce tankar ta kama da wuta jim kadan bayan ta yi hadari da misalin karfe 7 na Safiya a dai dai Lambe da ke kan hanyar zuwa Matogun dauke da litar man fetur dubu 54.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Lagos Mr Ibrahim Farinloye da ke bada tabbacin hadarin, ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa a ibtila’in, kuma tuni aka shawo kan wutar.

A cewar jami’in wutar da ta tashi ta kone gidaje 10 da ke gab da kan hanya, wanda ya haddasa asarar dukiya mai tarin yawa tare da juma dubunnan jama’a cikin fargaba.

Hadari ko kuma gobarar tankar mai ba sabon abu ba ne a sassan Najeriya musamman akan manyan hanyoyi la’akari da lalacewar titunan kasar da kuma ganganci direbobin da ke bin hanyoyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.