Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 17 sun mutu bayan karo tsakanin motar bas da tankar mai

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce wani hatsari da aka yi na taho mu gama tsakanin wata motar bas da tankar mai, yayi sanadin mutuwar mutane akalla 17, a yankin kudu maso yamacin jihar Ogun

Yadda wata tankar mai ta kone a Najeriya.
Yadda wata tankar mai ta kone a Najeriya. © Reuters
Talla

Shaheed Akiode na hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriyar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa hatsarin ya haddasa mummunan fashewar wani abu, zalika adadin wadanda suka mutu na iya karuwa, yayin da aka garzaya da wasu asibiti.

Jami’in ya ce lamarin ya faru ne a kan gadar Ishara da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

A watan Yunin da ya gabata, mutane 5 suka mutu, wasu 13 kuma suka jikkata a Legas, lokacin da wata tanka ta fashe saboda zubar iskar gas.

A watan Afrilu, mutane 12 suka mutu tare da konewar gidaje da dama, bayan da wata tankar mai ta kife, ta kuma zubar da man cikinta, sannan ta kama wuta a jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.