Isa ga babban shafi

Kotu ta mikawa Jam'iyyar PRP kujerar Majalisar wakilai a jihar Filato

Kotun da ke sauraren shari’ar zaben kujerar Majalisar wakilai na mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato a Najeriya ta soke zaben da aka yi wa Musa Agah na Jam’iyyar PDP, inda ta bukaci Hukumar zabe da ta bai wa dan takarar Jam’iyyar PRP Adam Muhammad Alkali shaidar zama wanda ya lashe zaben da aka yi na cike gurbi.

Wata mata yayin kada kuri'a a zaben na jihar Filato.
Wata mata yayin kada kuri'a a zaben na jihar Filato. AP - SUNDAY ALAMBA
Talla

Yayin gabatar da hukuncin yau juma’a, Mai shari’a Hope O. Ozoh da Khadi Usman Umar da Mai Shari’a Zainab M. Bashir sun bayyana cewar masu gabatar da kara daga PRP sun gabatar da kwararan shaidun da ke nuna cewar an tafka magudi wajen bai wa dan takarar PDP nasara.

Alkalan sun bukaci gaggauta mika takardar shaidar samun nasarar zaben ga dan takarar PRP Adam Muhammad Alkali da kuma rantsar da shi a matsayin dan majalisar tarayya.

Hukumar zabe ta kasa a Najeriya ta gudanar da zaben cike gurbin kujerar dan majalisar tarayya daga Jos ta Arewa da Bassa ne a ranar 26 ga watan Fabarairu na wannan shekara, sakamakon rasuwar dan majalisa Haruna Maitala wanda ke rike da kujerar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.