Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya fiye da 200 sun mika takardar ajiye aiki

Yayin da Najeriya ke tsakiyar yaki da ‘yan ta’addan boko haram da 'yan bindigar da suka hana jama’ar kasar zaman lafiya, rahotanni sun ce yanzu haka sojoji sama da 200 suka mika takardun su na ajiye aiki domin tube kakin su.

Wasu Sojin Najeriya da ke yaki da ayyukan ta'addanci da kuma hare-haren 'yan bindiga.
Wasu Sojin Najeriya da ke yaki da ayyukan ta'addanci da kuma hare-haren 'yan bindiga. CNBC Africa
Talla

Bayanai sun ce wadannan zaratan sojoji da suka gabatar da takardun su akasarin su, kanana ne wadanda su ke bakin daga domin fafatawa da 'yan ta’addan da suka addabi Najeriya.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya tabbatar da wannan labari na shirin barin aikin, a sanarwar da ya rabawa manema labarai yau asabar, bayan da wata jaridar kasar ta ruwaito cewar sojoji 243 suka gabatar da takardun ajje aikin ga shugaban su Laftanar Janar Faruk Yahya.

Sai dai Nwachukwu ya yi watsi da zargin cewar cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki na daga cikin dalilan da suka sanya sojojin gabatar da bukatar aje aikin.

Kakakin ya bayyana cewar irin wannan rahotan na bata suna na taimakawa wajen karyar gwuiwar sojojin da ke bakin daga, su na sadaukar da rayukansu domin kare Najeriya.

Nwachukwu ya ce gwamnatin Najeriya ta samar da kayan aiki na zamani ga sojojin da su ke yaki da yan ta’adda, yayinda kuma ake biyansu kudaden alawus akan kari saboda aikin da su ke wanda tuni aka fara ganin nasarar sa.

A karshe sanarwar ta ce shugaban rundunar sojin Janar Yahya ya godewa sojojin da za su ajje aikin akan gudummawar da suka bayar, tare da musu fatan alheri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.