Isa ga babban shafi

Bincike ya gano hannun Amurka a kuskuren harin Sojin Najeriya na 2017 a Borno

Wani binciken kwa-kwaf kan kuskuren harin sojin saman Najeriya a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Rann a jihar Borno na shekarar 2017 ya gano hannun Amurka wajen bai wa Sojin na Najeriya bayanan sirri da ya kai ga kaddamar da harin.

Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya.
Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya. © The Guardian Nigeria
Talla

Akalla fararen hula 160 ne galibi kananan yara suka mutu a kuskuren farmakin na watan Janairun 2017 wanda Sojin suka yi tsammanin dandazon mayakan Boko Haram ne a wajen.

Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito yadda wata jaridar Amurka ta shafin intanet ta wallafa wani rubutu a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata, wanda ke bayyana yadda Amurkan ta bayar da bayani ga Sojin Najeriya game da dandazon ‘yan ta’addan a Rann.

Jaridar ta yi ikirarin bankado wani sakamakon binciken Sojin Amurka da ke bayyana yadda sashen leken asirin kasar ya bayar da bayanan sirri ga Sojin Najeriyar don kaddamar da harin amma kuma ya zama kuskure ne wanda ya kai ga kisan fararen hular.

Bayan fitar hujjoji a sakamakon binciken da gwamnatin Amurka ta yi umarnin gudanarwa kan kuskuren harin wanda ya tayar da hankalin Duniya, jaridar ta ce an gano umarnin kaddamar da harin daga wani babban Janar din Sojin Amurka amma kuma aka gaza fitar da jawabin saboda kaucewa aikata ba dai dai ba daga kasar da ake gani a matsayin jagorar karfin Soji a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.