Isa ga babban shafi

Buhari ya jaddada alwashin ceto sauran fasinjan jirgin kasan Kaduna 31

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin ceto ilahirin fasinjan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mutum 31 da ‘yan bindiga suka sace, kalaman da ke zuwa watanni 5 bayan sace mutanen.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet © Presidency of Nigeria
Talla

Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar ta ruwaito, Muhammadu Buhari na cewa za su ceto mutanen tare da mayar da su cikin ahalinsu cikin koshin lafiya.

Wasu gungun ‘yan bindiga da basa ikirarin wata aqida ko addini, na ci gaba addabar hanyoyin arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya ta yadda su ke sace mutane don kudin fansa tare da kisa ba kakkautawa.

A ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata ne, ‘yan bindiga suka farmaki jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna tare da bude wuta inda suka kashe mutum 8 nan ta ke da kuma jikkata wasu 26 baya ga kwashe mutanen da ba a san adadinsu ba zuwa cikin daji.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito shugaba Buhari na cewa aikinsa ne tabbatar da kubutar da sauran mutum 31 da suka rage a hannun ‘yan bindigar ba tare da cutar da su ba.

A cewar Muhammadu Buhari sanin ‘yan Najeriya ne a kwanakin Sojoji na ci gaba da farmakar maboyar ‘yan bindiga da kuma kashe su baya ga ceto tarin mutanen da ke hannunsu, ya na mai cewa wannan kokari ba zai ragu b aba kuma za a dakata ba.

Muhammadu Buhari wanda matsalolin tsaro suka dabaibaye gwamnatinsa, y ace baza su dakata da fatattakar ‘yan ta’adda da batagari ba har sai an kai ga ganin karshensu tare da tabbatar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.