Isa ga babban shafi

Buhari ya gargadi 'yan Najeriya kan sake fuskantar yakin basasa a kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi al’ummar kasar da cewa kada su yarda a sake samun barkewar yakin basasa irin na shekarar 1967 zuwa 1970, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da ake samun baraka tsakanin al'ummar kasar ta yammacin Afrika dangane da abubuwan da suka shafi siyasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria presidency
Talla

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce son rai ne babban dalilin da ya haddasa yakin da ya lakume rayukan miliyoyin al’umma, sai dai ya jaddada cewar Najeriya za ta ci gaba da zama kasa daya dunkulalliya.

A lokacin da ya ke ganawa da tsofaffin shugabannin rusasshiyar jam’iyar CPC, ya ce an samar da jam’iyar ne bisa kishin kasa da kuma biyayya ga hadin kan Najeriya.

Shugaban ya bukaci dukkanin mambobin rusasshiyar jam’iyar ta CPC da sauran jagororin siyasa da a koda yaushe su maida hankali wajen samar da hadin kai da zaman lafiya da kuma kimar kasar.

Buhari ya yi la’akari da kudirin inganta rayuwar ‘yan Najeriya, wanda ya haifar da samar da jam’iyyar bai gurgunce ba, don haka ya bukaci ‘yan kasar su kara jajircewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.