Isa ga babban shafi

Rikicin PDP: Atiku da Wike sun amince da wani shirin sasantawa

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya, karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun amince da wani tsari na warware sabanin da ke tsakaninsu.

Atiku Abubakar kenan tare da Nyesom Wike
Atiku Abubakar kenan tare da Nyesom Wike © Daily Trust Aminiya
Talla

Sun cimma wannan matsaya ne a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Abuja a gidan tsohon ministan yada labaran kasar Jerry Gana.

Wannan dai shi ne karon farko da manyan ‘yan siyasar biyu su ka gana tun bayan da Atiku ya nada gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023.

Nadin dai ya harzuka Nyesom Wike, wanda ya kasance kan gaba a cikin sunaye uku da wani kwamiti ya ba da shawarar cewa dan takarar da jam’iyyar PDP sun kafa domin neman shawara kan zabin wanda zai tsaya a matsayin mataimakin Atiku.

Lamarin dai ya haifar da rikici a jam’iyyar, inda suma masu ruwa da tsaki ke korafin yadda shugabancin jam’iyyar ke yi wa Arewa katutu.

A wata tattaunawa da suka gudanar ranar Lahadi a Abuja, Mista Wike da magoya bayansa sun bukaci shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu da ya yi murabus daga mukaminsa, a wani bangare na sharuddan sulhu da Atiku.

Sai dai a wani taro da aka yi a ranar Talata, kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya kada kuri’ar amincewa da Mista Ayu yayin da kwamitin amintattu ya kafa kwamitin da zai gana da Mista Wike da abokan tafiyarsa

Sai dai kuma a ranar Juma’a a taron da Mista Gana ya jagoranta, shugabannin biyu sun amince da kafa wani kwamiti cikin sa’o’i 48 da zai taimakawa tsarin sasantawa a tsakaninsu.

Atiku da Wike sun amince su nada mutane bakwai kowannen su a cikin kwamitin, wanda zai duba dukkan batutuwan da bangaren Mista Wike ya gabatar tare da baiwa shugabannin biyu shawara kan yadda za a magance su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.