Isa ga babban shafi

Tsaro: Dole sojoji su yi bayani kan makudan kudaden da muka basu -Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bukaci sojojin kasar da su yi wa jama’a bayani akan irin makudan kudaden da gwamnati ta basu domin gudanar da ayyukan tsaro a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, tare da Babagana Monguno da kuma manyan hafsoshin tsaron kasar.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, tare da Babagana Monguno da kuma manyan hafsoshin tsaron kasar. © Buhari Sallau
Talla

Osinbajo ya ce jama’ar kasa na da hurumin sanin irin makudan kudaden da wannan gwamnati ta ware domin tinkarar matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya wanda ke kaiwa ga rasa dubban rayuka, dan kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar kalubalen tsaro.

Mataimakin shugaban kasar ya ce abin takaici ne kowanne lokaci idan anyi maganar tsaro, sai kaji wasu sojojin na cewa basu da kayan aiki, saboda haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsari wanda zai dinga bayyana irin kudaden da su ke kashewa a bangaren tsaro.

Osinbajo ya bayyana cewar ya dace ace Najeriya ta shawo kan matsalar 'yan bindigar da ake fama da ita ta wajen nuna kwarewa da kuma nuna dabarun yaki.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta gabatar da kasafin kudin tsaron da aka baiwa ma’aikatar tsaro tun shigowar gwamnatin Buhari a shekarar 2015 kamar haka:

2015 – Naira biliyan 968

2016 – Naira Triliyan guda da miliyan 700

2017 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 500

2018 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 350

2019 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 1 da 400

2020 – Naira Triliyan guda da miliyan dubu 800

2021- Naira Triliyan guda da miliyan dubu 960 da kuma kasafi na musamman Naira biliyan 722 da miliyan 530.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.