Isa ga babban shafi

Najeriya: an kama wadanda suka taimakawa 'yan bindiga harin kurkukun Kuje

Rohotanni daga Najeriya na cewa, jami’an binciken sirri sun kama wasu mutanen hudu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga 'yan bindiga da suka kai hari gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya, Abuja.

'Yan Sandan Farin kaya a Najeriya
'Yan Sandan Farin kaya a Najeriya guardian
Talla

Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa da ke tabbatar da kamen, tana cewa mutanen hudu sun yi kaurin suna wajen baiwa ‘yan ta’adda bayanai kan shige-da ficen da sauran al’amuran jami’an tsaro a Abuja.

Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na'urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu kirar China da basa amfani da intanet.

Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.

Hare-haren Abuja

Ana zargin Wadanda aka kama da taimakawa mahara da ke kai hari a wasu sassan yankunan Abuja.

Jaridar ta kuma rawaito cewa hukumar tsaro ta Najeriya na tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a matsalolin tsaro da hare-haren da ake kitsawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.