Isa ga babban shafi

Najeriya: Za ku yi hamdala idan kuka san halin da wasu kasashe ke ciki - Buhari

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya za su yi hamdala idan suka san halin da al’ummar wasu kasashe ke ciki.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Buhari ya yi wannan bayanin ne a yayin ziyarar da ya kai wa sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir Usman, a fadarsa a yau Asabar.

Shugaban ya ce zai cim gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da jin dadin ‘yan Najeriya, bayan da ya saurari korafi daga sarkin katsina da gwamnan Jihar, Bello Masari of Katsina.

Ya bukaci al’ummar kasar da su kara hakuri, yana mai cewa su na iya kokarinsu don sama musu sauki.

A nasa jawabin, gwamnaBello Masari ya bukaci ‘yan Najeriya da su taya shugaba Buhari da addu’a, inda ya ce jagorancin kasa mai al’ummomi dabam dabam ba abu ne mai sauki ba.

Masari ya ce wahalar da ake sha a kasar nan abu ne da ya shafi duniya gaba daya, yana mai cewa gwamnati n iya kokarinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.