Isa ga babban shafi

Gidajen Burodi fiye da 40 sun dakatar da aiki a Abuja saboda tsadar kayaki

Sama da kamfanonin yin Biredi 40 ne suka dakatar da aikinsu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Sakamakon tsadar kayayyakin yin Biredin, gami da dunbun Kudaden haraji da na wutar lantarki da suka ce suna biya. Lamarin da ya jawo wasu magidantan dake amfani da Biredin wajen karin kumallon, suka juya akalarsu ga Koko da Kosai.  Daga Abuja ga rahotan da wakilinmu, Muhammadu Kabiru Yusuf ya hada mana.

Farashin kayakin sarrafa burodi na ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya.
Farashin kayakin sarrafa burodi na ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya. REUTERS/Adama Diarra
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.