Isa ga babban shafi
Sudan

An kashe dalibi a zanga-zangar tsadar Burodi

Masu zanga-zanga da dama ne suka fantsama kan titunan Khartoum, babban birnin ƙasar Sudan da kuma yankin Darfur mai fama da rikici, inda suka rinƙa kona tayoyi da datse hanyoyi domin nuna fushin su kan tashin farashin Burodi.

Masu zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan.
Masu zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan. REUTERS/Stringer
Talla

Waɗanda suka shaida abinda ya faru sun ce ƴansanda sun rinƙa harba barkono mai sa hawaye a kan ɗaruruwan masu zanga-zanga a garuruwan Geneina da Nyala, da Darfur da kuma Damazin.

Hukumomi a Sudan sun ce an kashe ɗalibi ɗaya lokacin gudanar da zanga-zangar, yayin da gwamnan yammacin Darfur ya ce mutane 6 ne suka jikkata, amma yanzu haka ana kokarin shawo kan al’amarin.

Farashin Burodi ya yi tashin-gwauron-zabi bayan da gwamnati ta mayar da harkar shigo da garin fulawa cikin ƙasar a hannun ƴan kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.