Isa ga babban shafi

Farashin dabbobi ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya

Wannan na zuwa ne yayin da al'ummar musulmin duniya ke shirin gudanar da bukukuwan Sallah babba.

Raguna na da matukar mahimmanci ga musulmai a lokacin layya.
Raguna na da matukar mahimmanci ga musulmai a lokacin layya. ActuNiger
Talla

A irin wannan lokaci musulmi na gudanar da bikin yanka dabbobi, musamman raguna da sauransu a matsayin layya.

Sai dai a sassa daban-daban na Najeriya mutane na koka wa bisa hauhawar farashin dabbobin da ake samu, wanda ake ganin baya rasa nasaba da gabatowar bukukuwan Sallah babba.

Murtala Adamu Ibrahim ya leka wasu kasuwannin dabbobi da ke kudancin Najeriya ta cikin wannan rahoto da ya hada.

Latsa alamar kararrawa domin sauraron wannan sauti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.