Isa ga babban shafi

Buhari ya bayyana dalilin da ya hana shi cire tallafin man fetur

Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke kare matakin da gwamnatin sa ta dauka na bijirewa shawarar Hukumar Bada Lamuni ta Duniya wato IMF wajen cire tallafin man fetur a kasar, ya ce halin da wasu kasashe suka tsinci kan su sakamakon cire tallafin man fetur, izina ce ga Najeriya

Le président nigérian, Muhammadu Buahri, le 3 octobre 2019.
Le président nigérian, Muhammadu Buahri, le 3 octobre 2019. REUTERS - Siphiwe Sibeko
Talla

Yayin da yake amsa tambayoyi daga Jaridar Bloomberg, shugaban ya ce su kansu manyan kasashen duniya da suka cire tallafin yau suna yabawa 'aya zaki saboda illar da matakin da suka dauka ya haifar musu.

Buhari yace gwamnatinsa a shekarar da ta wuce ta 2021, ta kaddamar da shirin cire tallafin, amma bayan tuntuba mai zurfi daga masu ruwa da tsaki, da kuma halin da ake ciki a wannan shekara ta 2022, daukar matakin cire tallafin ba zai haifarwa kasar da mai ido ba.

Shugaban yace abinda ke gaban su shine bunkasa hanyoyin samar da tataccen man fetur a cikin gida da kuma baiwa yan kasuwa damar shiga harkar, domin dama wa da su wajen kafa manya da kananan matatun mai kamar irin su kamfanin Dangote da BUA da Waltersmith.

Rahotanni sun ce Najeriya ta kashe akalla naira triliyan hudu  karkashin wannan gwamnati, wajen biyan tallafin man fetur domin ganin jama’ar kasar sun sayi man cikin sauki.

Yanzu haka karancin man da kuma tsadar man dizil sun taimaka wajen samun hauhawar farashin kayan masarufi a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.