Isa ga babban shafi

Wani rahoto ya nuna yadda Najeriya ta ɗan samu ci gaba a zaman lafiya

Wani rahoton zaman lafiya na duniya da kungiyar Global Peace kan fitar duk shekara ya nuna yadda Najeriya ta koma matsayin ta 143 bana daga ta 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163.

Wani rahoton zaman lafiya na duniya da kungiyar Global Peace kan fitar duk shekara ya nuna yadda Najeriya ta koma matsayin ta 143 bana daga ta 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163.
Wani rahoton zaman lafiya na duniya da kungiyar Global Peace kan fitar duk shekara ya nuna yadda Najeriya ta koma matsayin ta 143 bana daga ta 146 a matakin zaman lafiya na duniya cikin kasashe 163. © Institute for Economics and Peace
Talla

Alkaluman na Global Peace ya nuna cewa Iceland ce kasar da ta fi zaman lafiya biye da New Zealand kana Ireland sai Denmark sannan Austria tukuna Portugal a ta 6 sai Slovenia da Czechia sannan Singapore da Japan a matsayin ta 10.

Najeriya

Najeriya ta matsa da maki 3 idan aka kwatanta da matakin da ta ke a bara, sai dai ta na kasan kasashe irinsu Mauritius da ke matsayi ta 28 a matakin zaman lafiya a duniya kuma ta 1 a Afrika, sai Ghana matsayin ta 40 kana Ganbia ta 45 sai Saliyo ta 50 da Equatorial Guinea ta 59 sannan Malawi ta 65 sai Senegal ta 70, Marocco ta 74 Rwanda 72 Liberia da Gabon na 75 Angola 78 kana Lesotho 100 kana Madagascar da Mozambique da kuma Namibia matsayin na 8 122 da kuma 68.

Sauran kasashen sun kunshi Zambia matsayin ta 56 kana Tunisia ta 85 sai Tanzania ta 86 kana Nijar ta 140 sai Burundi ta 131 da kuma Benin matsayin ta 105, Togo na matsayin ta 102 yayinda Mali ke matsayin ta 150 kana Libya a ta 151 da kuma Burkina Faso a matsayin ta 146 sai Habasha da Sudan matsayin na 149 da kuma 159.

Kasashe da suka fi fama da rikici

Kasashe mafi kololuwar rashin zaman lafiya kamar yadda alkaluman suka nuna su ne Afghanistan da Yemen da Syria da kuma Rasha kana Sudan ta kudu.

Kungiyar kan yin amfani da yanayin tsaron kasa ko rahoton hare-haren ‘yan ta’adda ko kuma yawaitar masu aikata laifuka gabanin fitar da alkaluman duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.