Isa ga babban shafi

Tinubu ya mikawa INEC sunan wanda zai taya shi takara a zaben 2023

Dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyya mai mulkin Najeriya APC a zaben dake tafe a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce ya mika sunan wanda ya zaba a matsayin mataimakinsa, ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC.

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin jam'iyyar APC Bola Tinubu.
Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin jam'iyyar APC Bola Tinubu. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ba kuma tare da ya bayyana sunan da ya gabatar ba.

Kafin wannan lokaci dai Tinubu ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga jihar Katsina ne a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakinsa domin ya cika wa’adin da hukumar INEC ta kayyade.

Sai dai an tsayar da Masari takarar ne na wucin gadi ne har zuwa lokacin da za a kammala tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, kan wanda za a tabbatarwa takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.