An nemi Najeriya ta binciki zargin hadin bakin soji da masu aikata muggan laifuka
Wata hadakar kungiyoyin fara hula a Najeriya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya kaddamar da bincike a kan zargin cewa wasu jami’an sojin kasar na hada baki da masu aikata muggan laifuka.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta ce hakan ya zama wajibi ne bayan kalaman da wasu matasa da suka gudanar da zanga zanga a karamar hukumar Umunneochi ta jihar Abia, da limamin cocin da aka sace, Samuel Kanu-Uche suka yi, inda suke zargin wasu bata garin sojoji da hannu a tabarbarewar tsaro a yankin.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da hadakar kungiyoyi 21 a karkashin jagorancin kungiyar nan mai da’awar mutunta doka, wato, Accountability Advocacy Centre, Lagos da ke Legas.
Kungiyoyin sun bayyana damuwa ainun, a kan yadda ake ci gaba da zargin sojoji da hannu a matsalar tsaro, suna mai kira da a gudanar da bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu