Isa ga babban shafi

Dakarun Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 14 tare da kubutar da mutane 100

Dakarun Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 14 tare da ceto sama da mutane 100 a wani samame da suka kai wasu mabuyan ‘yan ta’addan ISWAP dake kauyukan karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Dakarun Najeriya bayan sun samu galaba a kan ISWAP.
Dakarun Najeriya bayan sun samu galaba a kan ISWAP. AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY
Talla

Dakarun runduna ta musamman ta Operation hadin kai sun kain samamen ne a kauyukan Amdaga, Balazola, Ndakaine, Jango, Sabah da Gobara,duka  karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Baya  ga kashe ‘yan ta’adda 14 a yayin samamen, sun kama 15 daga cikinsu, suka kuma ceto iyalai 100 da suka hada da mata 33 da yara 67.

Daraktan yada labarai na ma’aikatan tsaron kasar, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga manema labarai a game da ayyukan sojin da ke gudana a yankin arewa maso gabashin Najeriya  a tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.

Dakarun gwamnatin sun kuma kwato wata mota kirar Toyota Hilux, wanda aka ce mallakin hukumar gyarar hanyoyin jihar Borno ce, wadda ‘yan ta’addan suka karbe a tsohuwar hanyar Marte a cikin watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.