Isa ga babban shafi

Gwamnatin Legas ta sake haramta sana'ar Okada

Gwamnatin Jihar Lagos da ke Najeriya ta sanar da haramta ayyukan yan okada a wasu kananan hukumomin Jihar daga ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa.

Wasu 'yan Okada a jihar Legas da ke Najeriya.
Wasu 'yan Okada a jihar Legas da ke Najeriya. REUTERS/Temillade Adelaja
Talla

Gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu ya ce dokar ta shafi kananan hukumomin Eti-Osa da Ikeja da Surulere da Lagos Island da Lagos Mainland da kuma Apapa.

Sanwo-Olu ya kuma bukaci manyan jami’an 'Yan Sandan da ke wadannan yankuna da su taimakawa hukumomin jihar Lagos wajen tabbatar da aiki da dokar.

Abu Yazidu na daya daga cikin Yan Okadan da wannan mataki ya shafa,  wanda a yayin zantawarsa da sashin Hausa na RFI ya bayyana cewar babu shakkah ana samun marasa da’a a cikinsu wadanda watakila karancin shekaru ke ingiza su karya dokoki.

Sai dai ya shawarci gwamnati da ta dauki wasu matakan na daidaita sana’ar tasu ta Okada a maimakon haramta ta baki daya, la’akari da cewar aikin na taka muhimmiyar rawa wajen zama hanyar dogaro da kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.