Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Okada sun soma ficewa daga Legas

Masu hayar babura da dama da aka fi sani da ‘yan Okada na ci gaba barin jihar Legas dake Najeriya, sakamakon soma aikin dokar haramta ayyukansu a wasu kananan hukumomi 6 da kuma manyan yankuna 9.

Wasu 'yan Okada akan hanyar marina dake jihar Legas a Najeriya.
Wasu 'yan Okada akan hanyar marina dake jihar Legas a Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Tun a ranar litinin 27 ga Janairun da ya gabata, gwamnatin Legas a Najeriya, ta haramta baburan hayar na Okada da kuma Keke Napep, babura masu kafa uku, dokar da ta ce ta shafi baburan kamfanonin sufuri na Opay da kuma Gokada.

Kididdiga ta nuna cewar adadin hanyoyin da dokar hana hayar baburan ta shafa ya kai akalla dubu 2, ciki harda manyan hanyoyi da kuma gadoji.

Daga cikin kananan hukumomin jihar ta Legas 15, da kuma manyan yankunan da dokar ta shafa, akwai, Apapa, Apapa Iganmu, Lagos Mainland, Yaba, Surulere, Itire Ikate, da Coker, da kuma Aguda.

Sauran yankunan sun hada da Lagos Island, Ikeja, Eti-Osa, Ikoyi da Obalende, Lagos Island ta gabas, sai kuma Ojodu, Onigbongo da kuma Iru Ikoyi zuwa Obalende.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.