Gumi ya kaddamar da kungiyar kare hakkin Fulani makiyaya
Shaharren malamin addinin Musuluncin nan dake Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya kafa kungiya da za ta kare hakkin Fulani makiyaya.
Wallafawa ranar:
Gumi ya sanar da kafa wannan kungiya da ya kira Nomadic Rights Concern, NORIC a takaice a yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a arewacin Najeriya.
Ya ce kungiyar za ta janyo hankali al’umma a game da cin zarafin Fulani makiyaya da ake yi.
Ya bayyan Farfesa Umar Labbo a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar, yana mai cewa NORIC za ta zama wata kafa da makiyaya za su kai korafe korafensu a game da abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya zuwa ga hukumomin da suka dace.
Ya kara da cewa makiyayan za su kai korafensu wajen kungiyar NORIC, wadda ita za ta taimaka musu ta wajen daukar mataki na shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu