Isa ga babban shafi
Najeriya - Yobe

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan garin Geidam

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan garin Geidam, da ke jihar Yobe, inda suka kutsa cikin garin a daren Larabar da ta gabata.

Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.
Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya. © FLORIAN PLAUCHEUR / AFP
Talla

Jaridar Daily Trust  ta ruwaito wasu da suka shaida faruwar al’amarin na cewa, mayakan na Boko Haram sun ajiye baburan nasu ne a wata unguwa nesa kadan da inda suka tafka barna.

Bayanai sun ce ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun afkawa wasu daga cikin mazauna yankin gabashin garin na Geidam ne, inda suka kona wata makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati, bayan kashe mutum daya a harabar makarantar.

Wata majiyar da Daily Trust ta ruwaito, ta bayyana cewarmayakan na Boko Haram sun kuma kai hari kan wani gidan mata masu zaman kansu a garin an Geidam inda suka kashe mutane akalla 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.