Isa ga babban shafi

Ya kamata Buhari ya fara sauraron wadanda basa cikin gwamnati - Mark

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya David Mark ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bude kofofin gwamnatin sa domin karbar shawarwari daga wajen jama’ar da basa cikin gwamnati domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya David Mark.
Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya David Mark. © Daily Trust
Talla

Mark yace wannan mataki ya zama wajibi ganin yadda matsalolin tsaron ke shan kan gwamnati, lura da cewar matsalar babu ruwanta da siyasa ko addini ko kuma kabila, sai dai bukatar ceto kasa baki daya.

Tsohon shugaban Majalisar yace cin amanar jama’a ne kawar da kai cewar al’amura suna tafiya dai dai, yayin da jama’a ke ci gaba da zama cikin ukubar rashin tsaro da kuma matsalolin tattalin arziki.

Mark yace duk wani mai hankali a cikin jama’a ya dace ya damu da halin da Najeriya ta samu kanta a yau da kuma zummar nazari domin lalubo hanyoyin da za’a bi domin shawo kan dimbin matsalolin da suka addabi kasar.

Tsohon shugaban majalisar ya kuma ce ita kanta gwamnati ya dace ta amsa cewar al’amura sun baci domin jagorancin yadda za’a gyara su, yayin da ya bayyana yakinin sa cewar ana iya shawo kan matsalolin muddin aka hada kai wajen aiki tare ba tare da nuna banbanci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.