Isa ga babban shafi
Najeriya - Falana

Falana ya roki Buhari ya yafewa duk barayin da ke gidan yari

Shaharerren Lauyan Najeriya, kuma mai kare hakkin bil’adama Femi Falana, ya yi kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya saki daukacin fursunonin da aka daure a gidan yari saboda samun su da laifin sata da wasu laifuka makamanta.

Hotunan taron Majalisar Zartaswa na Tarayya (FEC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar gwamnatin tarayya, Abuja. 13/04/22
Hotunan taron Majalisar Zartaswa na Tarayya (FEC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar gwamnatin tarayya, Abuja. 13/04/22 © Nigeria Presidency
Talla

Kiran na shi ya biyo bayan afuwar da Majalisar Koli ta Najeriya wadda ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da tsoffin manyan alkalai da shugaban kasa mai ci da gwamnonin jihohi sukayi wa wasu mutane 159 cikin su harda tosffin gwamnonin jihohin Filato Joshua Chibi Dariye da takwaransa na Taraba Jolly Nyame. 

Hotunan taron Majalisar Zartaswa na Tarayya (FEC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar gwamnatin tarayya, Abuja. 13/04/22.
Hotunan taron Majalisar Zartaswa na Tarayya (FEC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar gwamnatin tarayya, Abuja. 13/04/22. © Nigeria Presidency

Falana ya bayyana haka ne yayin jawabi a wani taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a otal din Sheraton dake birnin Legas, ranar Jumma’a

Yaki da Rashawa

Shaharerren lauya yace, bai kamata ace mutumin da yake ikirarin yaki da cin hanci da rashawa kuma yazo yana ahuwa ga barayi a kutu ta samasu da laifin sace biliyoyin dukiyar al’umma ba.

Sun fara yafewa kansu yanzu, Mutumin da ya ce ya zo yaki da cin hanci da rashawa ya rika yin afuwa ga mutanen da aka samu da laifin satar biliyoyin Naira".

Wannan ne yasa Falana ya bukaci shugaba Buhari ya saki daukacin fursunonin da aka tsare saboda sata, domin su ma ‘yan Najeriya ne, bai kamata a nuna musu banbanci ba.

Nuna Banbanci

A karkashin sashe na 17 na kundin tsarin mulkinsu, ya ce za a samu daidaito ga kowani ‘yan kasa sannan sashe na 42 ya ce ba za a nuna wariyar jinsi da makamantansu ba. Don haka bai kamata ku sallemi mutane biyu ku bar sauran a can ba”.

Yace, muddun gwamnati batayi haka ba to zai bai wa lauyoyi shawarar rugawa kotuna domin kalubalantar yadda aka nunawa wadanda suke karewa wariya.

Lauya Femi Falana mai fafutukar kare hakkin bil'adama a Najeriya
Lauya Femi Falana mai fafutukar kare hakkin bil'adama a Najeriya falana.jpg

Falana ya kara da cewa, idan har za’a iya sallamar manyan barayi da sunan afuwa, to mai zai hana suma kananan barayi da watakila suka saci taliya ko indomi don yunwar cikinsu samun wannan dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.