Isa ga babban shafi

Dattawan Najeriya sun ce Buhari ya sauka daga mulki saboda ya gaza

Kungiyar  Dattawan Arewacin Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya sauka daga mukamin sa saboda abinda ta kira kasa shawo kan kashe kashen jama’ar da akeyi a sassan kasar ba tare kaukautawa ba

shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Daraktan yada labaran kungiyar ta NEF Dr Hakeem Baba Ahmed yace gwamnatin Buhari bata da wata hanyar magance matsalolin tsaron da suka addabi kasar, saboda haka jama’ar Najeriya ba zasu ci gaba da zama a karkashin ikon masu kisa da garkuwa da mutane da fyade da kuma aikata wasu laifuffuka ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin gaisawa da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni. 20/8/2021.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin gaisawa da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni. 20/8/2021. © Buhari Sallau

Baba-Ahmed yace kundin tsarin mulki ya bada damar da shugabannin kan iya sauka daga mukaman su idan sun gaza cika alkawuran da suka yiwa talakawa ko kuma kasa kare rayuka da dukiyoyin su.

Daraktan yace lokaci yayi da shugaba Buhari zai yi nasari akan wannan mataki tunda jagorancin sa ya gaza samarwa jama’ar kasar tsaron da ake bukata.

Baba-Ahmed yace kungiyar ta su na sane da nauyin wannan shawara da kuma sanin cewar jama’ar kasar ba zasu ci gaba da zama a irin wannan yanayi ba har zuwa shekara mai zuwa da shugaban zai kawo karshen mulkin sa.

Daraktan yace Yan ta’adda sun fahimci cewar babu shugabanci a matakin kololuwar jagorancin kasar, shi ya sa suka samu karfin yin abinda suka ga dama da kuma samun karfin gwuiwar yin abinda suke so wajen cin amanar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.