Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ba ta taba yin shugaba mai nagartar Buhari ba – Masari

Gwamnan jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya, Aminu Bello Masari ya ce Najeriya ba ta taba yin shugaba mai nagartar Muhammadu Buhari ba tun da aka kirkiro ta.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari. © The Guardian Nigeria
Talla

Masari ya ce tun da  Turawan mulkin mallaka suka hade kudanci da arewacin Najeriya a shekarar 1914, Najeriya ba ta taba yin dacen shugaba mai nagarta ba, sai da ta samu Buhari.

Ya yi wannan  bayani ne a yayin da yake jawabi a gaban wani gangami na wadanda suka ci gajiyar shirin gwamnatin Najeriya na tattabatar da daidaito a wajen rabon albarkatun kasa ranar Asabar a Katsina.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da suka sha radadin ayyukan ‘yan bindiga da ke aikata laifin kisa da satar shanu, da cin zarafin mata da yara.

Sakamakon kamarin da matsalar ta yi ne ma, wani lokaci a baya gwamna Masari ya ce lamarin ya fi karfin hukumomin tsaron kasar, inda ya yi kira ga al’ummarsa su dau matakin kare kansu.

Dubban mutane ne dai ‘yan bindiga suka kashe, ko suka sace  su don karbar kudin fansa a jihar Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya tun da suka fara ayyukansu 'yan shekarun da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.