Isa ga babban shafi

Buhari ya nemi a kara kudaden tallafin mai zuwa naira tiriliyan 4

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar wakilan kasar daidaita kasafin kudi na matsakaicin zango don samar da Naira tiriliyan 4 da nufin sanya su a bangaren tallafin man fetur.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Cikin wata wasika da Buhari ya aikewa shugaban majalisar wakilan Femi Gbajabiamila, ya bukaci amfani da karin dala 11 da aka samu kan farashin kowacce gangar mai don cike gibin tallafin, wanda baya cikin kunshin kasafin kudin bana.

A cewar shugaban Najeriyar an ware Naira biliyan 442 ne kawai don tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar bana ta 2022 daga Janairu zuwa Yuni, amma saboda tashin farashin danyen mai, da kuma dakatar da shirin cire tallafin man kwata kwata, kasar za ta bukaci karin Naira tiriliyan 3 da biliyan 557 domin ci gaba da biyan tallafin.

A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur a shekarar bana ta 2022, matakin da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce ba zai dore ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.