Isa ga babban shafi
Najeriya - APC

Amaechi ya bayyana anniyar ya gaji Buhari a shugabancin Najeriya

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya sanar da aniyarsa ta takarar neman shugaban ƙasa a zaɓen 2023. 

Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi.
Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi. Premium Times Nigeria
Talla

Amaechi, wanda a lokuta daban-daban ya musanta cewa yana sha’awar takarar, ya bayyana anniyar sa ce wannan Asabar a filin wasa na Amiesimaka Fatakwal, yayin taron godiya ga jam’iyyar APC na Ribas.

Ya ce,

“Na tsaya a gabanku yau don bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba,"

 

Dadedwa a gwamnati

Amaechi ya kasance cikin gwamnati tun shekarar 1999, inda ya yi wa'adi biyu a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas (1999-2007), yayi wa’adi biyu na shekaru takwas a matsayin Gwamnan Ribas (2007-2015). Yana daya daga cikin ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nadawa a 2019.

Ana iya cewa daya daga cikin manyan ministoci, kuma jigo a jam’iyyar APC, saboda ya rike mukamin shugaban yakin neman zaben Buhari har sau biyu a 2015 da 2019.

Wasu 'yan takara

A halin da ake ciki bayaga Amaechi, tsohon gwamnan Legas Bola Tinubu da gwamnan Kogi Yahaya Bello duk sun ayyana aniyarsu da tsakaya takarar neman shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC, mai mulkin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.