Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Zaben 2023: Majalisar Dattijai ta yi watsi da bukatar Buhari

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar shugaban kasar Muhammadu Buhari na sake yi wa sabuwar dokar zaben kasar gyaran fuska wajen cire bukatar saukar duk wani mai rike da mukamin siyasa kafin shiga takarar zaben shekara mai zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban Majalisar dattijan kasar Sanata Ahmed Lawal tare da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da shugaban Majalisar dattijan kasar Sanata Ahmed Lawal tare da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila. © Daily Trust
Talla

'Yan majalisun sun bayyana rashin gamsuwarsu da bukatar yi wa dokar da aka yi wa lakabi da ‘Electoral Act 2022’ gyaran fuska da gagarumin rinjaye lokacin da aka karanta ta a karo na biyu.

Kafin bai wa 'yan Majalisun damar bayyana ra’ayin su, 'yan majalisun da dama sun bayyana rashin gamsuwar su da bukatar yi wa dokar gyara, yayin da suka bukaci Majalisar Dattawan da ta mutunta umurnin kotu wadda ta hana ta daukar duk wani mataki na sake fasalin dokar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon jiya ya bukaci Majalisun dokokin da su soke sashe na 84 sakin layi 12 na sabuwar dokar wanda ya ce ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasa.

Wannan sashen na kunshe da tanadin da ke cewa duk wani mai rike da mukamin siyasa dole ya sauka daga mukaminsa kafin tsayawa takarar zabe.

A ranar litinin da ta gabata, alkali Inyang Ekwo ya amince da bukatar da jam’iyyar PDP ta gabatar masa na cewa dokar zaben ta riga ta zama dokar kasa saboda babu dalilin yi mata gyaran fuska ba tare da bin matakan da shari’a ta gindaya ba.

Kotun ta bada umurnin hana shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ministan shari’a da kuma Majalisar dokoki cire wannan tanadi da ke bukatar masu rike da mukaman siyasa cewar ya zama wajibi su sauka daga mukaman su kafin tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.