Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun huce fushi kan masu ba wa jami'an tsaro hadin kai

A Najeriya, ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane 5, mazauna garin Rogoji  dake karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara a wani hari da suka kai a karshen wannan mako.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Da suke tabbatar da wannan al’amri, mazauna yankin sun ce ‘yan bindigan sun yi musu aika aikar ne a matsayin hukunci, sakamakon bai wa jami’an tsaro bayanai a kansu da suke yi.

Garin Rogoji  na da nisan kilomita 2 ne kawai daga kwaryar garin Bakura.

Majiyoyi sun ce mazauna garin sun taimaka wa jami’an tsaro da ‘yan banga sosai a wajen yaki da ‘yan ta’addan da suka hana su sakat a yankunan Lambar Bakura da Dogon Karfe.

Jaridar ‘Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa ta jiyo daga majiyoyi cewa ‘yan bindigan sun shiga garin ne da safiyar Alhamis a lokacin da al’umma ke shirin sallar asuba, duk da turjiya da suka gamu da ita, inda suka kashe mutane 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.