Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Barazanar ramuwa daga 'yan bindiga na daf da tada unguwa guda a Gusau

Mazauna unguwar Mareri Quarters da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara sun fita daga unguwar sakamakon tsoron hari daga ‘yan bindiga.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Kafafen yada labaran Najeriya sun ruwaito yadda ‘yan sa kai, da hadin gwiwar jami’an tsaro suka ceto shugaban hukumar sufuri ta jihar Zamfara Aminu Adamu (Papa), bayan da ‘yan bindiga suka sace shi da iyalansa.

Mazauna Unguwar ne suka sanar da ‘yan sintiri kan batun sace Papa da iyalansa, su kuma ba su yi wata wata ba suka shiga aikin ceton su.

Bayan da suka ceto su ne, suka sanar da jami’an tsaro,  wanda suka datse hanyoyin fita ga su ‘yan bindigan, lamarin da ya sa aka kashe 6 daga cikin barayin.

Wani mazaunin Unguwar ya ce akasarin makawaftansa ba sa kwana a gidajensu tun bayan aukuwar lamarin, don gudun abin da ‘yan bindigan ka iya aiwatarwa a matsayin ramuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.