Isa ga babban shafi
Najeriya-Noma

Farashin shinkafa zai sauka a kasuwannin Najeriya- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yiwuwar farashin shinkafa ya sauka a kasuwanni bayan kaddamar da Dalar shinkafa har 13 karkashin shirin tallafawa manoma don ciyar da kasa bisa jagorancin bankin CBN.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari © lailasnews
Talla

A yau talata shugaba Buhari ya jagoranci kaddamar da dalar shinkafar inda yayin jawabinsa a bikin budewar ya ce gwamnatinsa na daukar dukkan matakan da suka dace don saukaka farashin kayaki musamman na abinci da shinkafar a kan gaba.

Farashin shinkafa ya yi tashin doron zabi ne a Najeriya bayan matakin gwamnatin kasar na kulle iyakokinta da makwabta a shekarar 2019 ciki har da iyakar Seme da ta hadata da jamhuriyyar Benin .

A wancan lokaci dai gwamnatin Najeriya ta ce matakin kulle iyakar wani yunkuri ne na hana fasakwaurin kayaki da kuma karfafa gwiwar manoman cikin gida.

Bayanai sun ce dalar 13 an samar da duk guda daya daga gonakin shinkafa miliyan 1 da aka yi aikin nomanta a sassan Najeriya karkashin shirin tallafawa manoma na ABP da shugaba Buhari ya kaddamar a 2015 wanda CBN ya jagoranta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tun bayan hawansa mulki ya kalli matakin karfafa manoma don baza komar tattalin arziki zuwa dogaro da bangaren noma fiye da albarkatun karkashin kasa.

Acewar shugaban la’akari da halin da ake yanzu za a iya tabbatar da nasarorin da suka cimma a bangaren aiki ko kuma bunkasa Noma a sassan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.