Ambaliya ta mamaye gonakin shinkafa a Borno
Ambaliyar ruwa ta rutsa da daruruwan manoma a jihar Borno dake tarayyar Najeriya, inda ta lalata gonakin shinkafa masu yawan gaske.Kididdiga ta nuna cewar fadin kasar noman da ambaliyar ta mamaye ya zarta kadada dubu 2.Iftila’in ya zo ne a daidai lokacin da hare-haren mayakan Boko Haram suka hana mafi akasarin manoma a jihar ta Borno zuwa gonakinsu.Wasu dai na ganin cewa wannan ambaliya ba karamar barazana ba ce, la’akari da cewa za ta iya jefa jama’a cikin halin rashin abinci.Daga Maiduguri, Bilyamin Yusuf ya yi tattaki zuwa yankunan da lamarin ya shafa ya kuma aiko mana da rahoto akai.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ambaliya ta mamaye gonakin shinkafa a Borno
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu