Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun cafke mai cin naman mutane da mataimakansa a Zamfara

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar kame wasu mutane 4 da suka amsa laifukan ci da kuma sayar da naman mutane.

Jami'an tsaro a jihar Zamfara.
Jami'an tsaro a jihar Zamfara. AP - Ibrahim Mansur
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar ta Zamfara Muhammada Shehu, ya ce lokacin da suka kame mutanen an gano sassan jikin dan Adam da suka hada da makogoro, hanji da kuma idanu biyu.

Mutanen da aka cafke dai sun hada Abdullahi Buba, Ahmad Tukur, Aminu Baba da kuma Abdulshakur Muhammad, wadanda rundunar ‘yan sanda ta gabatar da su ga manema labarai a garin Gusau.

A lokacin da yake amsa tambayoyi, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce an ba shi kwangilar samo sassan jikin bil Adama ne a kan kudi Naira dubu 500, kuma ya aiwatar da mugun aikin kafin a kama shi.

Shi kuwa wanda ake zargi da zama mai sayan sassan jikin na dan Adam, Aminu Baba, ya amince da aikata laifin, inda ya kara da cewar, ya kan ci sassan jikin dan Adam kuma ya gano makogwaro a matsayin abinda mafi dadi.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan a Zamfara ta kuma sanar da samun nasarar kwace makamin roka da kuma bindiga bayan yin artabu da ‘yan ta’adda a wasu yankuna da ke karkashin Gummi, Bukkuyum da kuma Maru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.