Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da dubu 1 cikin shekarar 2021

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yadda dakarun kasar suka kashe ‘yan ta’adda fiye da dubu guda baya ga ceto fararen hula dubu 2 daga hannun batagari a yankin arewa maso gabashin kasar cikin shekarar 2021 da muke ban kwana da ita, dai dai lokacin wasu ‘yan ta’addan fiye da dubu 22 suka mika wuya.

Wasu Sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram.
Wasu Sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram. Pulse.ng
Talla

Wani taron manema labarai kan nasarorin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a 2021 da ministan yada labaran Najeriyar Lai Mohamed ya gudanar a jihar Lagos ya ce dakarun kasar sun yi nasarar fatattakar ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar kamar yadda shugaban ya alkawarta.

Acewarsa baya ga ‘yan ta’adda dubu 22 da suka yi saranda tare da mika makamansu ga gwamnati, an kuma kashe wasu fiye da dubu guda baya ga kwato tarin makamai masu hadari da bama-bamai da kuma tseratar da dubunnan fararen hula daga hannun Boko Haram da ISWAP.

Ministan labaran Najeriyar, ya ce duk da tsanantar matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasar a shekarar 2021 dakarunsu na iyakar kokari wajen kare rayukan fararen hula.

Lai Mohamed ya ci gaba da cewa, matsalar tsaro, tattalin arziki da kuma karancin kudaden tafiyar da gwamnati da Najeriya ta fuskanta cikin shekarar nan, dukkaninsu gwamnati ta tafiyar da su cikin tsanaki tare da lalubo bakin zaren.

Acewarsa jagorancin Sojin da shugaba Buhari ya sauya ya taka rawar gani a magance matsalolin tsaron da kasar ta gani a baya, ko da ya ke matsalolin da annobar covid-19 ta haifar ya haddasa matsin rayuwa ga ‘yan kasa.

Ministan ya ce gwamnatin Buhari ta tunkari matsalolin da covid-19 ta haifar ta fuskar tattalin arziki bayan samar da tarin shirye-shiryen saukaka rayuwa, karkashin manufofinta na kudi da kuma gwarzantakarta a yakar cutar a bangaren manufofinta na Lafiya.

Ministan yada labaran na Najeriya Lai Mohamed ya kuma godewa al’ummar kasar kan goyon bayansu ga shugaba Muhammadu Buhari wanda ke da fatan barin kyakkyawar manufa ga kasar mai cike da tsaro da kuma zaman lafiya.

Ministan ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna goyon baya ga jami’an tsaron kasar da ke sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.