Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar Kwastam ta kama kwantena makare da bindigogi a Legas

Rahotanni daga jihar Legas a tarayyar Najeriya sun ce jami’an hukumar Kwastam da ke tashar jiragen ruwa ta Tin can, sun kama wata kwantena makare da bindigogi.

Wasu makamai da hukumar Kwastam ta kama a Najeriya.
Wasu makamai da hukumar Kwastam ta kama a Najeriya. Nigeria Customs Service
Talla

Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya cewa da fari wanda ya mallaki kwantenar ya shaidawa jami’an na Kwastam cewar na’urorin Talabijin ne kirar zamani a ciki, to amma bayan gudanar da bincike aka gabo adadin muggan bindigogin masu yawa a ciki.

Kawo yanzu dai babau karin bayan kan yawan bindigogin da kwantenar da aka kama ta kunsa, har sai an kammala gudanar da bincike, domin bankado wanda ya mallaki makaman.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami’an tsaron Najeriya ke kama manyan kwantenoni makare da makamai ba a tashohin jiragen ruwan kasar da ke jihar Legas, domin kuwa a watan Janairun shekarar 2017, jami’an Kwastam suka kame tarin makaman da yawansu ya kai a iya rabawa bataliyar soji.

Adadin bindigogin da aka kama a shekarar ta 2017 dai ya kai 661 boye cikin akwatuna 46, cikin wata kwantena mai tsawon kafa 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.