Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

An gudanar da bukukuwan nada Yusuf Buhari Talban Daura

An gudanar da bukukuwan nada Yusuf Buhari, ’dan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa dake Jihar Katsina.

Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawal da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Talban Daura Yusuf Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Gamduje
Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawal da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Talban Daura Yusuf Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Gamduje © Nigeria presidency
Talla

Bikin da aka gudanar a birnin Daura ya samu halartar mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal da Gwamnonin Jihohi da ministoci da kuma wasu fitattun jama’ar kasar.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sarkin Daura da kuma Gwamnan Katsina Aminu Belo Masari wajen bikin nadin Yusuf Buhari Talban Daura
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sarkin Daura da kuma Gwamnan Katsina Aminu Belo Masari wajen bikin nadin Yusuf Buhari Talban Daura © Daily Trust

Sarkin Bichi dake Jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda yake siriki ga Yusuf Buhari na daga cikin Sarakunan da suka halarci bikin.

Bikin nadin sarautar ya gamu da suka daga sassan jama’a saboda halin da kasar ke ciki na rashin tsaro, musamman kashe kashen da aka samu a makwannin da suka gabata.

Masu tsokaci akai na cewar ya dace a dage bikin zuwa wani lokaci nan gaba domin samun kwanciyar hankali musamman a yankin arewa maso yammacin kasar cikin su harda jihar Katsina inda ‘Yan bindiga ke kai munanan hare hare suna kashe talakawa.

Wasu mahaya dawaki wajen bikin
Wasu mahaya dawaki wajen bikin © Daily Trust

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci bikin ba saboda tafiyar da yayi kasar Turkiya domin halartar taron shugabannin Afirka da na kasar da aka fara jiya juma’a wanda ake sa ran kammala shi a yau asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sarkin Daura Umar Faruk Umar na cewar sun yanke hukuncin nada Yusuf Talban Daura ne domin hana shi ci gaba da zama a Abuja da Yola bayan mahaifin sa ya kammala wa’adin mulkin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.