Isa ga babban shafi
NAJERIYA

Wata babbar mota ta kashe dalibai 13 a Lagos

Akalla daliban makarantu 13 ake fargabar sun mutu yau a birnin Lagos dake Najeriya lokacin da wani direban babbar mota ya afka musu bayan sun tashi daga makaranta.

Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci asibiti domin ganin halin da yake ciki a watanni baya
Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci asibiti domin ganin halin da yake ciki a watanni baya © Premium Times
Talla

Bayanan dake zuwa mana na nuna cewar, an samu hadarin ne akan hanyar Isheri dake kusa da tashar ’Yan Sandan Ojodu, abinda ya haifar da katse zirga zirgan ababan hawa a hanyar da kuma boren matasa.

Wasu shaidun gani da ido sun ce katsewar birki ne yayi sanadiyar samun hadarin, yayin da direbar motar yayi kokarin tserewa bayan aukuwar lamarin.

Matasan cikin fushi sun kai hari ofishin ‘Yan Sandan Ojodu wadanda suka kama direbar motar suka tsare shi, abinda ya sa su amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin tarwatsa su.

Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos Adekunle Aisebutu ya tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da yace suna kokarin tantance adadin yaran da hadarin ya ritsa da su da kuma gudanar da bincike akan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.