Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

An tsinci gawarwakin wasu 'yan Nijar 7 a Lagos

A Najeriya, an tsinci gawarwakin wasu 'Yan asalin Jamhuriyar Nijar guda 7 da ke zaune gida daya a unguwar Alaba da ke birnin Legas da sanyin safiyar wannan Lahadi.

An tsinci gawarwakin wasu 'yan Nijar 7 a unguwar Alaba dake birnin Lagos
An tsinci gawarwakin wasu 'yan Nijar 7 a unguwar Alaba dake birnin Lagos © Rfi hausa - Ahmed Abba
Talla

Bayanai sun ce ba wasu alamun raunuka a jikin mutanen 7 da suka mutu, wadanda tuni aka yi masu jana'izarsu tun da safiyar, bayan sanar da 'yan sanda faruwar lamarin. 

Shugaban 'Yan Nijar mazauna Legas Alhaji Sa'idu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, to saï dai kawo yanzu ba a gano dalilin mutuwar mutanen 7 ba, inda ya ce tuni suka sanar da mahukunta ciki har da ofishin karamin jakadan Jamhuriyar Nijar da ke Legas. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.